Vinicius Junior ne ya zura wa Madrid kwallo daya a raga ya kuma zama silar zura kwallo ta biyu a ragar Girona a karawar da suka doke Real Madrid/Hoto:Reuters

Dan wasan Real Madrid da Brazil, Vinivicius Junior, ya nuna rashin jin dadinsa kan alkanci a gasar LaLiga bayan an hukunta shi don korafin da ya yi bayan an yi masa ba abin da yake ganin bai dace ba a karawar Real Madrid da Girona.

Minti 36 da fara wasa dan wasan bayan Girona, Santiago Bueno, ya bugi Vinicius da kwallo yayin da dan wasan ke kwance a kasa. Da Vinicius ya yi korafi a kan hakan sai alkalin wasan ya nuna masa katin gargadi.

Ba a san abin da Vinicius ya gaya wa alkalin wasan ba a karawar da Girona ta doke Real Madrid da ci 4-2.

Sai dai bayan wasan, Vinivius ya fitar da wani sako a shafinsa na Twitter da ke nuna cewa alkalin wasan bai yi daidai ba inda ya wallafa kalmar LaLiga cikin alamar dariya.

Masu sha’awar kwallon kafa a shafukan sada zumunta sun yi suka ga wadanda suka ce sun yi amfani da kalmar “mono” wadda ke nufin biri a filin wasan yayin da aka bai wa Vinicius katin gargadi.

Wariyar launin fata a gasar La liga ba bakon abu ba ne ga Vinicius Junior/Hoto:Reuters

An sha yi wa dan wasan na Real Madrid miyagun kalamai na wariyar launin fata a gasar ta LaLiga.

TRT Afrika da abokan hulda