Vincent Aboubacar ne ya zura wa Kamaru kwallo a ragar Brazil a karawar da kasarsa ta doke Brazil a Gasar Kofin Duniya da aka yi a bara

Fitaccen dan wasan Kamaru Vincent Abubakar ya taimaka wa Besiktas wajen doke Fernabahce a karawar da suka yi ranar Lahadi.

Fitaccen dan wasan na Kamaru ya zura kwallon karshe a fafatawar da kungiyarsa ta buge Fernabahce da ci 4-2.

Kwallon da ya ci a minti na 91 ita ta bai wa Besiktas nasara a gwabzawar da suka yi a gidan Fernebahce.

Jaridun kasar Turkiyya sun ambato Vincent yana cewa dole shi da sauran ‘yan wasan Besiktas su yi irin bajintar da suka yi domin su yi nasara bayan sun rasa dan wasa daya.

Aboubacar ya ce suna yi wa dan wasan bayan tawagar Turkiyya mai taka leda a Besiktas, Tayyip Talha, wanda ya ji ciwo a karawar fatan alheri.

Ya kara da cewar nasarar da Besiktas ta samu ta Tayyip Talha ce.

A watan Janairun bana ne dai Vincent Aboubacar ya koma taka leda a Besiktas a karo na uku.

Ya taba buga wasan aro a kungiyar a shekarar 2016.

Daga baya ya rattaba hannu a yarjejeniya da kungiyar a watan Satumbar 2020.

Sai dai bai dade a kungiyar ba inda ya tafi Alnassr ta Saudiyya a watan Yunin 2021.

Da Cristiano Ronald ya koma kungiyar ta Saudiyya kuma, Aboubacar ya bar Alnassr a farkon wannan shekarar inda ya sake komawa Besiktas.