Cristiano Ronaldo mai shekara 38, ya zama dan kwallon da ya fi taka wa kasarsa leda a duniya yayin da buga wasanni 198, bayan wasan da ya buga wa kasarsa Portugal da ta samu nasara kan Luxemburg da ci 6 da nema.
Wannan ya sa ya zama dan wasan da ya fi taka wa kasarsa leda a wasan kwallon kafa na maza a duniya.
Dan wasan wanda ya samu kyautar Ballon d'Or sau biyar, ya sha gaban Bader Al-Mutawa na tawagar kwallon kafa ta kasar Kuwaiti wanda ya yi wasanni 196 tun shekarar 2022.
Ya buga wasansa na 197 a makon da ya gabata a karawarsu da Liechtenstein a wasan neman shiga gasar UEFA EURO.
Yana cikin ‘yan wasa kadan da suka samu kyautar Ballon d’Or da Gasar Zakarun Turai sama da sau biyar, kuma har ila yau shi kadai ne dan wasan da ya zura kwallaye sama da 800 a raga cikin wasa 1100.
Ronaldo ya kasance dan wasan da ya fi mabiya a a shafukan sada zumunta inda yake da mutum miliyan 513 ke bin sa a shafin Instagram.