A gasar Kofin Duniya ta 2022, Maroko ta kai matakin dab da na karshe, kafin Faransa ta fitar da ita da ci 2-0. / Hoto: AFP

A wata sanar da ta ba da mamaki, hukumar kwallon kafa ta duniya, wato FIFA, ta ayyana kasashen Maroko da Sifaniya da Portugal a matsayin masu masaukin gasar kwallon kafa ta duniya, wadda za ta gudana a shekarar 2030.

Sannan kasashen Uruguay da Argentina da Paraguay za su karbi bakuncin wasannin farko na bude gasar, don bikin cika shekaru 100 da fara ta, a cewar sanarwar da FIFA ta fitar ranar Laraba.

FIFA ta ce kasashen uku Moroko da Portugal da Sifaniya su kadai ne suka gabatar da neman damar daukar nauyin gasar a shekarar ta 2030. A badi ne FIFA ya kamata ta ayyana kasar da za a buga gasar.

An fara buga gasar ta FIFA ne a shekarar 1930 a kasar Uruguay, inda mai masaukin bakin ta lashe gasar, bayan doke kasar Argentina a wasan karshe da aka buga a garin Montevideo.

Sifaniya ta shiga rukunin kasashen ne, duk da cewa 'yan makonni ne bayan da shugaban kungiyar kwallon kafa ta kasar, Luis Rubiales, ya yi murabus bayan shan matsin lamba sakamakon zargin sumbatar leben 'yar wasan kasar, Jenni Hermoso lokacin gasar Kofin Duniya ta mata.

Kasa ta biyu a Afrika

Maroko za ta zamo kasa ta biyu a Afirka da za ta karbi bakuncin gasar cin Kofin Duniya na kwallon kafa karkashin jagorancin Fifa, bayan kasar Afirka ta Kudu da ta karbi bakunci a shekarar 2010.

Sarkin Maroko, Mohammed VI ya yi maraba da kukuncin na FIFA. Kasar Maroko da ke yankin Afirka ta ba da mamaki lokacin gasar bara a Qatar, inda ta zamo kasar Afirka ta farko da ta kai matakin dab da na karshe a gasar.

Hukuncin na FIFA shi ne karo na farko da za a gudanar da gasar kofin duniya a nahiyoyi uku, kuma a kasashe shida, wanda zai sanya a buga wasannin mataki daban-daban a mabambantan yanayi da yankunan duniya.

Gasar ta baya a shekarar 2022 ta gudana ne a Qatar, kuma Argentina ce kasar da ke rike da kofin a yanzu.

TRT Afrika