Dan wasan gaban na Portugal ya koma kungiyar Al Nassr da ke Saudiyya a 2023 bayan ya bar Manchester United. Hoto/Getty Images

Shahararren dan wasan kwallon kafa na duniya Cristiano Ronaldo ya ce yana da burin cin kwallo dubu daya kafin ya yi ritaya daga taka leda.

Ya bayyana wannan kudurin ne bayan shugaban kungiyar kwallon kafa ta FC Porto Nuno Pinto ya kalubalance shi kan hakan.

Ronaldo ya ci kwallonsa ta 857 a wasan da kasarsa ta Portugal ta buga da Slovakia inda aka ta shi 3-2.

Ana dai kallon wannan sabon burin da dan kwallon ya bijiro da shi a matsayin wata alama da ke nuna ba lallai ya yi ritaya daga kwallon kafa a halin yanzu ba.

Rahotanni sun ce Ronaldo ya nuna sha’awarsa ta sake tsawaita kwantiragi da kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya har zuwa 2027.

Wannan na nufin dan wasan wanda ya ci gasar Ballon d’Or sau biyar zai iya halartar wasan Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026 wadda Amurka da Canada da Mexico za su karbi bakunci.

TRT Afrika da abokan hulda