Ronaldo shi ne dan wasan da ya fi ci mata wasa a kakar da muke ciki inda ya zura kwallo shida./Hoto:  Al Nassr

Cristiano Ronaldo ya ci kwallo ta 850 a tarihinsa na kwallon kafa a wasan da Al Nassr ta doke Al-Hazm da ci 5-1 a gasar Saudi Pro League ranar Asabar.

Ronaldo ya zura kwallonsa ta shida a wasanni uku da ya buga a baya-bayan nan sannan ya taimaka aka zura kwallo biyu a yayin da Al Nassr ta yi nasara sau uku a jere a gasar lig.

Shi ma Sadio Mane ya zura kwallo a wasan.

"Mun sake yin bajinta! Muna ci gaba da kwarewa. Mu ci gaba da tafiya @AlNassrFC...na ci kwallo 850 a tarihina kuma ina ci gaba da murza leda!” a cewar Ronaldo, mai shekara 38, a sakon da ya wallafa a soshiyal midiya.

Al Nassr na bayan kungiyar Al-Hilal da maki hudu a gasar lig bayan ta yi rashin nasara a wasanni biyu a wannan kakar wasa.

Ronaldo shi ne dan wasan da ya fi ci mata wasa a kakar da muke ciki inda ya zura kwallo shida, yayin da tsohon dan wasan Liverpool Mane yake biye da shi da kwallo biyar.

Reuters