Frank Lampard ya amince ya zama kocin Chelsea na rikon kwarya daga yanzu zuwa karshen kakar wasa ta bana.
A ranar Laraba tsohon kocin kungiyar ta Chelsea ya yarda ya koma jagorancin ta shekaru sama da biyu bayan an sallame shi daga aiki.
Lampard ba shi da aiki tun bayan da aka sallame shi daga Everton a watan Janairu kasa da shekara daya da zuwansa kungiyar.
A watan Janairun 2021 Chelsea ta kore shi daga aiki inda ta maye gurbinsa da Thomas Tuchel.
Ranar Lahadi kungiyar ta kori Graham Potter daga aiki bayan shi ma ya maye gurbin Tuchel.
Chelsea na matsayi na 11 a Gasar Firimiya ta Ingila kuma ta tashi 0-0 a wasan da suka yi da Liverpool ranar Talata a Stamford Bridge.
Tana bayan kungiyoyi hudu da ke saman teburin Firimiya da maki 14, duk da cewa ta kashe sama da Fam miliyan 550 a bana don sayo sabbin ‘yan wasa.