Mutum fiye da 50,000 ne suka mutu sakamakon girgizar kasar da ta auka wa larduna 11 na Turkiya a watan Fabrairu. Madrid / Photo: Reuters

Atletico Madrid za ta fafata da Besiktas a makon gobe domin samun kudin da za a taimaka wa mutanen da girgizar kasa ta shafa a Turkiyya.

"Za mu zo birnin Istanbul. Za mu yi wasa domin samun kudin da za a taimaka wa wadanda girgizar kasa ta shafa," in ji Atletico Madrid a sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Asabar.

Kungiyar ta Sifaniya da ke buga gasar La Liga ta tabbatar da cewa za a yi wasan a filin Vodafone Park da ke Istanbul ranar Laraba da misalin karfe shida da rabi na yamma a agogon Nijeriya da Nijar.

Besiktas ta wallafa sako a shafinta na intanet inda ta ce za a soma sayar da tikitin wasan ranar Lahadin nan, kuma za a yi amfani da kudin wurin sake gina makarantu a yankunan da girgizar kasa ta yi wa barna.

Mutum fiye da 50,000 ne suka mutu sakamakon girgizar kasar da ta auka wa larduna 11 na Turkiya a watan Fabrairu.

AA