Hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai, UEFA ta fara bincike kan wani alƙalin wasa na Ingila David Coote, bayan bayyanar wani bidiyo da aka ce ya nuna shi yana shan hodar ibilis, wanda aka ce an ɗauka ne lokacin gasar Euro da ta gabata.
UEFA ta ce ta ƙaddamar da bincike kan alƙalin da tuni aka dakatar da shi a Ingila a gasar Firimiya, bayan fitar wani bidiyon daban da ya nuna shi yana faɗan munanan kalamai kan tsohon kocin Liverpool, Jurgen Klopp.
A farkon makon nan ne hukumar kula da alƙalan wasa ta Ingila, PGMOL ta dakatar da alƙali Coote mai shekaru 42, don yin bincike kan wancan bidiyon.
Sai dai a yanzu Coote zai fuskanci wani binciken na daban bayan an kwarmata wani sabon bidiyon da yake nuna shi yana shaƙar wani abu da ya yi kama da koken, yayin gasar Euro 2024 da aka yi a Jamus.
Bidiyon ya nuna wani da ke kamanni da David Coote yana zuƙar 'farin gari' ta hanci, ta amfani da takardar dalar Amurka da aka nannaɗe.
Kafin dakatar da shi a Ingila, Coote yana aiki a matsayin alƙalin wasa a gasar Firimiya a matsayin ƙwararren mai duba bidiyo yayin wasa.
Yau Alhamis UEFA ta bayyana cewa ta umarci jami'inta na ɗa'a da ladabtarwa ya duba ya gani ko Coote ya saɓa Dokokin Ɗa'a na hukumar.
Alƙalin zai cigaba da nisantar filin wasa a wasanni cikin Ingila da kuma tsakanin ƙasashe, har sai an kammala bincike-binciken da ake yi kansa.
Masu saka ido kan al'amuran wasanni suna ganin da wuya David Coote ya iya dawo kan aikinsa na alƙalancin wasa, sakamakon wannan badaƙala da ya shiga.