Benzema ya shafe shekara14 yana murza leda a Real Madrid inda ya nuna bajinta sosai. Hoto.Getty

Real Madrid ta tabbatar da cewa dan wasan gabanta Karim Benzema zai bar kungiyar bayan shafe shekara 14 yana taka leda inda bayanai suka ce zai tafi kungiyar Al Ittihad ta Saudiyya.

"Real Madrid da Kkaftin dinmu Karim Benzema mun amince a kawo karshen zamansa mai cike da hakaza wanda ba za a manata da shi ba a wannan kungiyar tamu," a cewar wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Lahadi.

Gidan talbijin na gwamnatin Saudiyya Al Ekhbariya ya rawaito cewa dan wasan, mai shekara 35, ya amince da kwantaragin shekara biyu "mai tsoka" da kungiyar Al Ittihad.

Bayanai sun nuna cewa kwantaragin ta kai $107.05 m (€100 m) kuma tuni dan wasan ya nuna shaukinsa na tafiya can.

Benzema zai hadu da tsohon abokin murza ledarsa a Real Cristiano Ronaldo wanda a halin yanzu yake buga wasa a kungiyar Al Nassr.

Dan wasan, wanda ya taba cin kyautar Ballon d’Or, ya ci Gasar Zakarun Turai ta Champions League sau biyar sa’annan ya ci La Liga sau hudu a Real Madrid.

Kungiyar ta kuma ce za ta shirya taron bankwana ga Benzema a ranar Talata inda ake sa ran shugaban kulob din Florentino Perez ya halarci taron.

Benzema ya soma taka leda a Real Madrid kuma shi ne mutum na biyu da ya fi cin kwallo a tarihin kungiyar inda ya ci kyaututtuka da dama.

TRT Afrika da abokan hulda