Manchester City ce ta dauki kofin gasar a 2023 bayan ta doke Inter Milan a filin wasan Ataturk da ke birnin Santambul na Turkiyya. Hoto/Getty Images

Bayan shafe watanni uku ana hutu, Gasar Zakarun Nahiyar Turai, a ranar Talata ake sa ci gaba da gasar ta UEFA inda AC Milan za ta fafata da News Castle sa’annan Young Boys su fafata da Leipzig.

Manchester City wadda ita ce zakarar gasar UEFA a 2023 ta kafa tarihi a kakar da ta gabata ta hanyar zama zakara a karon farko bayan ta lallasa Inter Milan a filin wasa na Ataturk da ke Istanbul.

City din ce kungiyar kwallon kafa ta shida daga kasar Ingila wadda ta taba cin wannan gasar bayan Manchester United da Liverpool da Nottingham Forest da Aston Villa da Chelsea.

Tsawon shekaru, kungiyoyi 23 suka lashe Gasar Zakarun Nahiyar Turai. Real Madrid ce a kan gaba inda ta ce gasar sau 14, daga ciki har da wasan gasar na farko da aka soma tsakanin 1955 zuwa 1956.

Kofi na baya-bayan nan da suka ci shi ne a 2022 inda suka kara da Liverpool a wasan karshe suka doke su. Sa’annan AC Milan ta kasance kulob din da ya fi samun nasara a Italiya inda kulob din ya ci kofin sau bakwai sai Liverpool da Bayern Munich suka ci gasar sau shida kowanensu.

AA