Turkiyya ta ci kwallon farko lokacin da Zeki Celik ya bugo bal ta kasa sai dan Wales Chris Mepham ya tura ragarsa, amma sai VAR ta ceto Wales ta soke kwallo. / Hoto: Reuters

Turkiyya ta haye saman teburin rukunin D na neman shiga gasar Euro 2024, bayan ta doke Wales da ci biyu da nema, duk da cewa ta barar da fenareti tare da rasa kwallaye biyu ta alkalancin VAR.

A wasan da aka buga ranar Litinin a garin Samsun na Turkiyya, 'yan wasan kasar biyu, Mehmet Umut Nayir da Arda Guler su suka zura kwallaye biyu a ragar Wales. A yanzu Turkiyya tana da maki tara a wasanni hudu.

Bayan buga wasanni hudu zuwa yanzu, Wales suna da maki hudu ne kacal, kuma suna mataki na hudu a teburin.

Wales ta rasa dan wasanta daya a minti 41 da fara wasa, a lokacin da Joe Morrell ya far ma Ferdi Kadioglu, lamarin da ya janyo korar dan wasan.

Turkiyya ta ci kwallon farko lokacin da Zeki Celik ya bugo bal ta kasa sai dan Wales Chris Mepham ya tura ragarsa, amma sai VAR ta ceto Wales ta soke kwallo.

Dan wasan Inter Milan, Hakan Calhanoglu, ya samu fenareti a minti 64 da fara wasa , amma mai tsaron gidan Wales, Danny Ward, ya doke kwallon. Bayan wasu mintuna, dan wasan Turkiyya Nayir ya zura kwallo a raga, amma aka soke kwallon.

Turkiyya ba ta daina kokarin zura kwallon a ragar Wales ba, amma sai a minti 72 ne Nayir ya zura kwallo a ragar Wale, duk da cewa golan Wales, Ward, ya yi kokarin tankwabe kwallon.

Daga bisani Guler ya tabbatar da nasarar Turkiyya da kwallo ta biyu da ya zura a raga, da kafarsa ta hagu.

TRT Afrika