Turkiyya ta samu gurbin zuwa Gasar UEFA EURO 2024 bayan ta doke Latvia 4-0

Turkiyya ta samu gurbin zuwa Gasar UEFA EURO 2024 bayan ta doke Latvia 4-0

Turkiyya ce ta farko a Rukunin D da maki 16 lamarin da ya sa ta samu gurbin  zuwa Gasar EURO 2024.
Dan wasan gaban Turkiyya Cenk Tosun (an zagaye shi) ana taya shi murna bayan ya zura kwallonsa ta biyu wadda ta sa aka tashi da ci 4-0 tsakanin Turkiyya da Latvia a wasan neman cancantar zuwa gasar UEFA Euro 2024 a Rukunin D a Filin Wasa na Konya Buyuksehir Belediye a Konya.  /Hoto: AFP

Turkiyya ta samu gurbin zuwa gasar Zakarun Turai ta 2024 UEFA bayan ta doke Latvia da ci 4-0 a wasan da suka fafata ranar Lahadi.

Bayan an kammala minti arba'in da biyar na farko ba tare da an zura kwallo ba, 'yan wasan Turkiyya sun dawo da kuzarinsu daga hutun rabin lokaci a wasan da suka yi a Filin Wasa nan Konya Metropolitan Municipality.

Yunus Akgun ne ya soma zura kwallo a minti na 58, yayin da Cenk Tosun ya zura kwallo ta biyu a minti na 84.

Kerem Akturkoglu ya ci kwallo ta uku a minti na 88, sannan Tosun ya sake cin kwallo a minti na 92.

Wannan sakamakon ya nuna cewa Turkiyya ce ta farko a Rukunin D da maki 16 lamarin da ya sa ta samu gurbi a Gasar EURO 2024.

Sifaniya ta doke Norway da ci 1-0 bayan Gavi ya zura kwallo a minti na 49 abin da ya sa suka zama na farko a Rukunin A da maki15 inda su ma suka samu gurbin zuwa EURO 2024.

TRT World