Tsohon dan wasan tsakiyar Faransa Sofiane Diop ya koma taka wa Maroko leda daga yanzu kuma an sanya sunansa a cikin tawagar ’yan wasan da za su buga wasan neman gurbin shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta shekarar 2026.
Dan wasan mai shekara 23 wanda yake buga wasa a kungiyar Nice ta Faransa wasa a matsayin dan wasan tsakiya, ya zabi ya buga wa Maroko wasa duk da cewa zai iya zabar ya buga wa kasar Senegal.
Kocin Maroko Walid Regragui ya bayyana sunan shahararren dan wasan a cikin ’yan wasa 25 da ya zaba a ranar Alhamis don tunkarar kasashen Eritrea da Tanzaniya.
Zabar Diop ba ta zo da mamaki ba saboda dan wasan ya taba buga wa tagawar matasa ta Faransa kuma ya dade da cacantar buga wa Maroko da Senegal wasa. “Na dade ina magana da Sofiane tun lokacin da na zama koci,” in ji Regragui a ranar Alhamis.
“Ya dade da zabar Maroko amma bai koma nan ba saboda wasu tsare-tsare da kuma raunin da ya yi,” a cewar kocin.