Kwamitin wasannin Olympics ne ya zabi Antetokounmpo bisa amincewar al'umma./ Hoto: Antetokounmpo      

Tauraron wasan kwallon Kwando, ɗan asalin Nijeriya da Girka Giannin Antetokounmpo zai zama baƙar fata na farko da ya zai rike tutar ƙasar Girka a faretin bude wasannin Olympics na bana, a cewar masu shirya gasar.

Ƙasar Girka wadda a al'adance ita za ta jagoranci faretin bude wasannin Olympics na bana, ta bai wa Antetokounmpo damar zama daya daga cikin 'yan wasa na farko da za su fara bude gasar a birnin Paris.

Antetokounmpo mai shekaru 29, wanda ya kasance ɗan wasa mafi tsada a fagen kwallon kwando har sau biyu, zai riƙe tutar Girka tare da ɗan wasan tsere Antigoni Ntrismpioti mai shekaru 40, a birnin Paris a ranar 26 ga watan Yuli.

An zabi Antetokounmpo ne bisa amincewar al'umma, yayin da Ntrismpioti ya yi nasara ta hanyar kada kuri'u, kamar yadda kwamitin Olympics na Hellenic, wanda shi ne hukumar Olympics ta Girka ya sanar.

Tauraron da ke haskawa

Antetokounmpo, wanda ake yi wa lakabi da ''Greek Freak,'' ƙwararren ɗan wasan kwando na Milwaukee Bucks a Ƙungiyar kwallon kwando ta Ƙasa (NBA) a Amurka.

A shekarar 2016 zuwa 2017, ya zama ɗan wasa na farko a cikin fagen manyan wasanni biyar don samun gurbi na jimullar maki 20.

A 2017, ya samu lambar yabo ta ɗan wasa mafi ƙwarewa sannan an zabe shi a matsayin kyafytin na All-Star a shekarar 2019 da 2020 da kuma 2023.

TRT Afrika