Mauricio ne ya fara kai Spurs wasan karshe na gasar zakarun Turai/Hoto:Reuters

Tattaunawa tsakanin Chelsea da tsohon kocin Tottenham, Mauricio Pochettino, mai shekara 51 ta yi nisa.

Rahotanni na cewa Chelsea na son bai wa dan kasar Ajentina damar maye gurbin Graham Potter da ta kora a farkon watan nan bayan ya rike kulob din na tsawon watanni.

Duk da cewa ba a sani ba ko Pochettino zai karbi aikin nan take ko kuma za a bar Frank Lampard ya ci gaba da rikon kwarya, bayanai sun ce dan Ajentinan yana son aikin.

Wadanda suke son dan Ajentinan mai shekara 51 ya jagoranci Chelsea suna ganin ya yi abin azo a gani da kungiyar Spurs a lokacin da ba ta kashe wani kudi mai yawa ba/Hoto:Reuters

Tun da farko Pochettinoa ya ki amincewa da tayin da Chelsea ta yi masa, amma da aka yi masa alkawarin karin iko kan kungiyar fiye da zaban ‘yan wasa kawai sai ya yarda a ci gaba da tattaunawa.

A da ana sa ran kocin zai koma kungiyarsa ta da, Spurs, bayan Antonio Conte ya bar kulob din a watan Maris, amma yanzu da abokiyar hamayyar Tottenham, Chelsea yake tattaunawa.

Chelsea ta fara magana da kocin Bayern Munich, Julian Naglesmann kafin ta mayar da hankalinta kan Pochettino.

Tsohon kocin Sifaniya da Barcelona, Luis Enrique, ya kasance cikin wadanda kulob din ke so a da tare da kocin Burnley, Vincent Kompany, wanda ya horar da kungiyar gasar Firimiya a wannan kakar.

Watanni bayan Pochettino ya kai Spurs wasan karshe na gasar Zakarun Turai ne aka sallame shi daga kungiyar/Hoto:Reuters

Tun bara ne Pochettino ba shi da aiki bayan ya bar PSG.

Pochettino ya kasance kocin farko da ya fara kai Spurs wasan karshe na gasar Zakarun Turai a 2019 inda Liverpool ta doke ta ci biyu da nema.

Sai dai ‘yan watanni bayan wannan tarihin da ya kafa aka sallame shi daga kungiyar.

A 2021 ne Mauricio ya koma PSG a matsayin koci.

Tunanin magoya baya

Tun da rahotannin suka fara kan batun mutane suka fara bayyana ra’ayoyinsu.

Yayin da wasu ke ganin Pochettino zai taka rawar gani a Chelsea, wasu na nuna damuwa kan dacewarsa.

“Pochettino ya fi Enrique da Nagelsmaa idan ana maganar Chelsea. Ya fi dacewa da mu,” in ji wani mai goyon bayan Chelase, Janty a shafinsa na Twitter.

Shi kuwa Jayjay cewa ya yi a shafinsa na Twitter: “Irin uzurin da suka yi wa Potter suke yi wa Pochettino. Sun ce ya yi narasar da ta wuce tsammani a Spur, abin da suka fada game da Potter kenan a Brighton. Kuskure iri daya. Ba za su gaya mana ya kware a dabarun kwallo ba ko kuma ya lashe wannan ko wancan kofin ba.”

Ko ya dace ko bai cancanta ya zama kocin Chelsea ba, masu kungiyar ne za su yanke hukunci.

TRT Afrika da abokan hulda