Shugaban Mauritania Mohamed Ould Ghazouani ya lashe zaɓen shugabancin ƙasar da ya gudana ranar 29 ga Yuni, kamar yadda sakamakon kashi 99.15 na rumfunan zaɓe da hukumar zaɓen ƙasar ta saki zuwa ranar Lahadi ya nuna.
Sakamakon da aka wallafa a shafin intanet na hukumar zaɓen Mauritania ya nuna cewa an sake zaɓar Ghazouani da kashi 56 na ƙuri'un.
Hakan ya ba shi tazara kan abokin karawarsa, ɗan rajin kare haƙƙin ɗan'adam, Biram Dah Abeid, wanda hukumar ta Ceni ta yi hasashen zai lashe kashi 22 na ƙuri'un.
Abeid ya faɗa ranar Lahadi cewa ba zai amince da sakamakon "hukumar Ceni ta Ghazouani" ba.
Ya ce, "Za mu amince da namu sakamakon kaɗai, don haka za mu fita tituna don yin watsi da ƙirgen hukumar zaɓen".
Sai dai ya ce matakin nasu zai kasance "na lumana", inda ya yi kira ga sojoji da jami'an tsaro "ka da su bi umarnin gwamnati".
Da maraicen Lahadi, jami'an tsaro sun yi ƙawanya a hedkwatarsa ta 'yan hamayya, cewar wani ɗan jaridar AFP.
Maus sa-ido na AU, EU
Ɗaya mai takara da shugaba Ghazouani, wanda shi ne shugaban jam'iyyar Tewassoul, Hamadi Ould Sid' El Moctar, a halin yanzu lissafi ya nuna yana da kashi 13 na ƙuri'un.
Ya ce zai ci gaba da "kasancewa mai mayar da hankali" kan ko za a samu duk wata kaucewa dokokin zaɓe.
An ƙiyasta jimillar yawan fita zaɓen ya kai kashi 55.
Zaɓen 2019 ne ya kawo shugaba Ghazouani kan mulki, inda a karon farko aka samu miƙa mulki daga zaɓaɓɓiyar gwamnati zuwa wata zaɓaɓɓiyar, tun bayan samun 'yancin kai daga Faransa a 1960, da kuma jerin juyin mulki daga 1978 zuwa 2008.
Yayin da yankin Sahel ya fuskanci jerin juyin mulki da ƙazantar hare-haren 'yan ta'adda, musamman a Mali, Mauritania ba ta fuskanci hari ba tun 2011.
Ghazouani ya mayar da hankali kan taimakawa matasa, a ƙasar da take da al'umma miliyan 4.9, inda kusan kashi uku cikin huɗu suke rukunin ƙasa da shekara 35.
Shekara guda da ta gabata, 'yan hamayya sun yi inkarin zaɓen 'yan majalisa da kakkausar murya, wanda jam'iyyar Ghazouani ta lashe.
Tarayyar Afrika ta tura tawagar mutane 27 a matsayin masu sa-ido da ba su daɗe a can ba, yayin da Tarayyar Turai ta tura ƙwararru kan zaɓe su uku.
Gwamnatin Mauritania ta kafa hukumar kula da zaɓe ta ƙasa, wadda 'yan hamayya suka soka a matsayin wata hanyar kankane ƙuri'u.