Asusun Kula da Arzikin Saudiyya ya kaddamar da wani sabon kamfanin saka hannayen-jari na wasanni don janyo "manyan shirye-shiryen wasanni a duniya" zuwa ga masarautar.
Ya dauki wannan mataki ne a yayin da kasar ke ci gaba da sayen shahararrun 'yan wasan kwallon kafar duniya.
Kamfanin mai suna, SRJ Sports Investments, "zai zuba jari wajen samar da kuma kirkirar sabbin shirye-shiryen wasanni na Intellectual Property (IP) da harkokin kasuwanci da fitattun manyan gasa na wasanni da kuma karbar bakuncin manyan shirye-shiryen wasannin duniya a Saudiya ,"a cewar wata sanarwar da Asusun saka hannayen-jari na al'umma (PIF) ya fitar.
Kamfanin ''zai mayar da hankali ne kan sana'o'in da suka kware wajen samar da ayyuka na musamman na magoya baya da sauya fasalin fasahar wasanni da kuma karfafa matsayin Saudiyya ta hanyar sanya kasar a kan gaba a harkokin wasanni da nishadi a duniya.''
Sabunta Masarautar
Fannin wasanni ya kasance daya daga cikin fannonin da masarautar mai arzikin man fetur ta sanya a gaba a kokarinta na ganin ta na ganin ta mayar da shi harkar kasuwanci da yawon bude ido a duniya karkashin shirin samar da sauye-sauye na 2030 wanda Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman kuma shugaban shirin PIF ke bi.
Kungiyoyin kwallon kafa a yankin Gulf da suka yi fice wajen fitar da danyen man fetur a duniya, sun kulla yarjejeniya da fitattun 'yan wasan kwallon kafa, farawa da Cristiano Ronaldo a bara, sai kuma Karim Benzema da Jordan Henderson da Sadio Mane a bana, duk da cewa ba a yi nasara wajen daidaitawa da Kylian Mbappe da Lionel Messi ba.
Kazalika Saudiyya ta girgiza duniya da wasan da aka buga na Golf bayan irin kudaden da ta zuba a wasan kungiyar LIV da kuma daukar nauyin gasar Formula One Grand Prix.
Haka kuma kasar ta mayar da hankali kan kungiyar ATP da WTA da ke gudanar da wasannin Tennis na maza da mata, inda ta shirya wasan baje-kolin na manyan 'yan wasa maza a wajen birnin Riyadh a bara.
Asusun PIF na daya daga cikin manyan shirye-shiryen bunkasa arzikin kasa da ake da shi a duniya inda yake da kadarori na sama da dala biliyan 620.