Bayan da ɗan wasan Liverpool Mohamed Salah ya lashe kyautar gwarzon wata a Gasar Firimiya a karo na shida a watan Nuwamba, ya yi daidai da adadin da Cristiano Ronaldo da Steven Gerrard suka kafa a baya.
Tauraron ɗan wasan ɗan asalin Masar ya lashe kyautar gwarzon watan ne bayan ya ci ƙwallaye biyar cikin bakwai da Liverpool ta ci a gabaɗaya watan na Nuwamba.
Tun bayan zuwansa Liverpool a shekarar 2017, Salah ya ci jimillar kyautukan har shida a wannan rukuni na bajinta a babbar gasar ta Ingila.
Zuwa yanzu ya ci jimillar ƙwallaye 168 a Liverpool a wasannin Gasar Firimiya, wanda ya sa ake ganin ya kama hanya kafa sabbin tarihin bajinta.
A yanzu Salah ya kamo tarihin bajinta da gwarzon ɗan wasan Liverpool Steven Gerrard ya kafa na lashe kyautar sau shida, kuma babu wani ɗan wasan Liverpool da ke da yawan kyautukan ban da su biyun.
Bugu da ƙari, Salah ya yi kankankan da gwarzon tsohon ɗan wasan Manchester United Cristiano Ronaldo, a yawan kyautukan na gwarzon wata.
Kamo Kane da Aguero
Wannan bajinta da Salah ya nuna ya sa ana kallon abin da ya rage masa shi ne kamo tarihin bajinta da Harry Kane da Sergio Aguero suka kafa na lashe kyautar har karo bakwai.
Hakan zai faru da zarar Mohamed Salah ya sake lashe kyautar ta gwarzon wata a karo guda, inda zai ba shi jimillar kyautuka bakwai, daidai da tsofaffin 'yan wasan na Firimiya.
Tsohon ɗan wasan Tottenham Harry Kane, da tsohon ɗan wasan Manchester City Sergio Aguero sun tara jimillar kyaututtuka bakwai a gasar a baya.
Duk da cewa Salah zai iya barin Liverpool a ƙarshen kakar bana a bazarar 2025, ana ganin zai iya kamowa da doke tarihin 'yan wasan biyu, har ma ya kafa nasa sabon tarihin.