A ƙarshe dai, tauraron ɗan wasan nan ɗan asalin Faransa, Kylian Mbappe ya koma Real Madrid ta Sifaniya. An kwashe watanni ana raɗe-raɗin zuwansa Madrid, amma sai a wannan makon ne ya tabbatar da zuwansa Madrid.
Bayan jin wannan labari ne tsohon gwarzon ɗan wasan Madrid, wanda a yanzu yake buga wa Al Nassr ta Saudiyya wasa, Cristiano Ronaldo ya aika wa Mbappe saƙon fatan alheri.
Tun asali dai, Mbappe ya ɗauki Ronaldo a matsayin abin koyinsa tun yana ƙaramin yaro mai sha'awar ƙwallo. Haka nan Mbappe bai ɓoye burinsa na son taka leda a Real Madrid ba.
Bayan kawo ƙarshen kwantiraginsa a PSG ta Faransa, Mbappe ya koma Madrid a Litinin ɗin nan, a hukumance.
Mbappe ya wallafa wani hoto a shafinsa na Instagram, inda ya nuna shi yana ƙarami sanye da rigar Madrid, da kuma hoton gwaninsa Ronaldo a bayansa. Daga nan ne Ronaldo ya amsa masa inda ya aika masa saƙon fata na gari.
Ronaldo ya yi tsokaci da cewa "Yanzu zan yi [kallo]. Ina farin cikin ganin ka haskaka Bernabeu. #HalaMadrid". Saƙon ya faranta wa dubban masoyan Madrid a faɗin duniya.
Masoyan na Madrid za su yi fatan ganin Mbappe ya bi sahun Ronaldo a Madrid, wanda ya ci ƙwallaye 450 da tallafin ƙwallo 131 a wasanni 438 da ya buga wa Madrid, kuma ya ci kofuna 16 a shekaru tara, da kyautar gwarzon duniya sau biyar.
Sai dai a yanzu Mbappe zai fara atisaye ne da tawagar ƙasar Faransa, gabanin fara gasar cin kofin ƙasashen Turai da za a yi a Jamus. Ba zai buga wa Madrid wasa ba, sai an zo wasannin sharar fage inda za su kai ziyara Amurka.