Baya ga Cristiano Ronaldo da Lionel Messi kungiyoyin kwallon kafar Saudiyya na neman manyan ‘yan kwallo 50, in ji wani rahoton da kafar ESPN ta wallafa.
Rahoton ya ce a wani yunkuri na mayar da Saudiyya kasar da za ta rika jan hankali a fagen kwallon kafa, tana son ta sayo manyan wasan kwallon kafa daga kungiyoyin gasar Firimiya ta Ingila da Seria A da La Liga da Bundesliga da kuma la Liga ta Portugal.
Rahoton ya kara da cewa ‘yan wasan da ake nema su ne ‘yan wasan da kwantiraginsu ya kare a Turai saboda kasar ta zama inda ‘yan kwallo za su rika zuwa bayan Turai.
Kasar Saudiyya, wadda za ta karbi bakuncin gasar zakarun nahiyoyi ta kwallon kafar duniya a watan Disamba, tana son ta mika takardar neman karbar bakuncin gasar Kofin Duniya ta 2030.
Shiga gasar ‘Fro Lig’ ta Saudiyya da Cristiano Ronaldo ya yi ta daga darajar gasar a duniya inda masoya dan wasan da ya fi ko wane dan wasa mabiya a shafukan sada zumunta suke bin wasansa.
Bayan Ronaldo ya bai wa duniyar kwallon kafa mamaki inda ya koma taka leda a Al Nass daga Manchester United, ana sa ran Messi ma zai tafi Al Hilal da ke a Saudiyya.
Shirin na sayen ‘yan wasan da ke taka leda a kasashe irin su Ingila da Faransa da Jamus da Italiya da kuma Sifaniya ya samu goyon bayan ma’aikatar wasanni ta Saudiyya, kamar yadda ESPN ta rawaito.
Baya ga Messi, manyan ‘yan wasan da kwantiraginsu ya kusa karewa sun hada da Roberto Firminsho na Liverpool da Ilkay Gundogan na Manchester City da Adama Traore na Wolves da kuma Yerry Mina da Aboulaye Doucoure na Everton.
Duk da cewar ana sa ran Karim Benzema ya tsawaita kwantiraginsa a Real Madrid, dan wasan bai rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya a Benabeu ba tukuna.
Majiyoyin da suka yi magana da ESPN sun ce matsalar tattalin arzikin da kungiyoyin kwallon kafa a Turai ke fuskanta ta zama wata dama ga gasar ‘Fro Lig’ din Saudiyya, in ji rahoton.