Roberto Calenda, ejan ɗin tauraron ɗan wasan Napoli ɗan asalin Nijeriya, Victor Osimhen ya yi gargaɗin cewa, “Victor ba haja ba ce da za a kai wata uwa duniya don a samu sabbin hannu a gurbin da ya bari”.
Shahararren ɗan jaridar wasanni Fabrizio Romano shi ya wallafa wannan labari a shafukansa na sadarwa.
“Victor yana da sauran aiki a Turai. Osimhen ɗan wasan Napoli ne, kuma yana da kwantiragi da ya sabunta ba daɗewa cikin aminci," in ji Calenda.
Kalaman na ejan ɗin tamkar suka ne kan yadda Napoli take ɗaukar batun barin Osimhen, kuma alama ce ta cewa ba za su amsa tayin tafiyarsa Saudiyya ba a yanzu.
Ejan ɗin ya ƙara da cewa Osimhen ya kafa tarihi a Napoli kuma ya ci kyautar gwarzon ɗan wasan shekara na Afirka. Duk lokacin da aka samu tayin sayensa, a kullum muna karɓar hukuncin kulob ne.
Osimhen bai buga wasannni biyun farko na Napoli ba a gasar Seria A, amma an ce bai karɓi tayin tafiya ƙungiyar Al-Ahli ta Saudiyya ba, inda rahotanni ke cewa ya fi ƙaunar ci gaba da buga wasa a Turai.
Rufe kasuwar 'yan wasa
Sai dai ya rage 'yan kwanaki kafin a rufe kakar cinikin 'yan wasa da za ta kammala ci ranar 30 ga watan Augustan nan.
An sha danganta ɗan wasan mai shekaru 25 da ƙungiyoyi kamar Chelsea da PSG, amma sai aka ruwaito cewa ƙungiyar Al-Ahli ta Saudiyya tana dab da cim ma yarjejeniyar sayen Osimhen kan Euro miliyan 65 (dala miliyan 72).
Rahotanni sun bayyana cewa kwantiragi tsakanin Al-Ahli da Napoli "tana dab da kammaluwa, in bacin ƙananan bayanai".
A cewar Fabrizio Romano, Osimhen yana neman a ba shi 'albashi na musamman', sannan a sanya saɗarar cewa zai iya barin kulob ɗin a cikin kwantiragin.