Eden Hazard ya sanar da yin ritaya daga tamaula

Eden Hazard ya sanar da yin ritaya daga tamaula

Kwallaye takwas ya ciyo wa Madrid a shekara hudun da ya yi a can.
Hazard ya taba kasancewa keftin din kasar Belgium:Hoto/Reuters

Tsohon shahararren dan wasan Chelsea da Real Madrid Eden Hazard ya ce ya yanke shawarar yin ritaya daga buga kwallon kafa, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Instagram a ranar Talata.

Dan wasan Belgium din, mai shekara 32, ya kasance ba shi da kungiya tun bayan da ya bar kungiyar Real Madrid a kakar bana. Akwai rahotannin da ke cewa ya samu tayin koma wa wasu kungiyoyi, amma sai ya zabi ya yi ritaya.

"Wajibi ne ka tsaya ka yi nazari kuma ka dakata a lokacin da ya dace. Bayan shekara 16 kuma na buga fiye da wasanni 700, na yanke shawarar yin ritaya a matsayina na dan wasan kwallon kafa a matakin kwararru. Na cimma burina, na yi wasa kuma na samu nishadi a lokuta daban-daban a filaye a fadin duniya," in ji Hazard.

Dan wasan ya yi ritaya ne bayan ya kasa taka rawar a zo a gani a shekara hudun da ya yi a Real Madrid.

Ya koma can ne bayan da ya lashe kofunan biyu da Chelsea kuma ya zura kwallaye 110 a wasanni 352 da ya buga mata.

Ya koma can ne bayan da ya lashe kofunan biyu da Chelsea kuma ya zura kwallaye 110 a wasanni 352 da ya buga mata.

TRT Afrika