Neymar ya ci kwallo biyu a wasan da  Brazil ta doke Bolivia da ci 5-1 a wasan da suka fafata a Belem./Hoto:Reuters

Neymar ya zama dan wasan da ya fi ci wa Brazil kwallo a tarihi bayan ya zura kwallaye biyu a wasan da suka doke Bolivia ranar Juma'a.

Hakan na nufin dan wasan ya ci wa kasarsa kwallo 78 kuma ya doke tarihin da Pele ya kafa.

Dan wasan na gaba, wanda ya yi wa Brazil wasa sau 125, ya zura kwallo biyu a ragar tawagar Bolivia a wasan neman cancantar shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta Kasashen Kudancin Amurka.

Brazil ta doke Bolivia da ci 5-1 a wasan da suka fafata a Belem.

Kwanakin baya ne tsohon dan wasan na Barcelona, mai shekara 31, ya bar Paris Saint-Germain zuwa kungiyar Al Hilal ta kasar Saudiyya.

Pele, wanda ya rasu a watan Disamba yana da shekara 82, ya ci wa Brazil kwallo 77 a wasanni 92 da ya buga wa kasar daga 1957 zuwa 1971.

AFP