Keftin din Argentina Lionel Messi ya ci kwallonsa ta 100 ga kulob dinsa da ke rike da Kofin Duniya a lokacin da kulob din ya lallasa kasar Curacao da ci 7-0.
Dan wasan wanda ya ci Ballon d’Or sau bakwai ya soma cin ragar kasar da ke tsibirin Caribbean a minti na 20 a Santiago del Estero a ranar Talata.
Wannan na zuwa ne shekara 17 bayan ya soma ci wa Argentina kwallo a wasa tsakanin Ajantina da Croatia a Maris din 2006 inda aka tashi 3-2.
Dan wasan mai shekara 35 ya kara cin wata kwallon jim kadan bayan shiga minti na talatin da soma kwallon inda kuma ya ci ta ukun a minti na 37.
Wannan ne karo na bakwai da dan wasan ke cin kwallaye uku a wasa guda ga kungiyar kwallon kafa ta kasar Argentina.
“Babu wasu kalmomi da za su iya bayani kan Messi,” kamar yadda Nicolas Gonzalez ya bayyana.
“Ya fi kowa a duniya kuma yana nuna haka wasa bayan wasa, rana bayan rana. A duk lokacin da ya taba kwallo, sai ya saka murmushi.”
Messi ya shigo wannan wasan ba wai a matsayin wanda ya fi kowa cin kwallo ga kasarsa ba, amma da kwallayen da suka zarta jumullar wadanda suke bin shi a yawan cin kwallaye ga Ajantina –– Gabriel Batistuta mai kwalllaye 56 da kuma Sergio Aguero mai 41 idan aka hada ba su kai yawan na Messi ba.
Wannan ne wasa na biyu da Ajantinaa ta buga tun bayan da ta ci wasan cin kofin duniya a Qatar inda ta cire Faransa da ci 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan an tashi 3-3.