Beckham ya je kallon Messi a lokacin da yake atisayensa na farko a filin kulob din Inter Miami. Hoto/Reuters

Daya daga cikin masu kungiyar Inter Miami, David Beckham, na ganin Lionel Messi na bukatar karin lokacin kafin ya saba da sabuwar gasar Major League Soccer, yana mai cewa yanayin wasan ya sha bamban da na wasan Turai.

Beckham, tsohon dan wasan Manchester United da Real Madrid, ya je kallon Messi a lokacin da ya halarci atisayensa na farko a kulob din a ranar Talata bayan dan wasan ya saka hannu kan kwantiragi na shekara biyu da rabi.

Dan wasan tsakiya na Sifaniya Sergio Busquets, wanda tsohon abokin wasan Messi ne tun daga Barcelona, shi ma ya yi atisaye a filin kulob din bayan kulla yarjejeniya a ranar Asabar, tare da tsohon kocin Barcelona da Argentina Gerardo ‘Tata’ Ma rtino wanda shi ne ke horar da su.

“Duk yadda yake da kyau da karfi, Leo da Sergio na bukatar lokaci domin su saba da wannan wurin,” kamar yadda Beckham ya bayyana.

“Za su iya ba ku mamaki, akwai yiwuwar mu iya samun nasara a kowane wasa, amma dole ne mu yi hakuri,” in ji shi.

Akwai bukatar magoya bayan Miami su nuna irin wannan hakuri a yayin wasan da za a buga a ranar Juma’a da kungiyar Mexico Cruz Azul, kuma Beckham ya ce ba lallai ba ne dan wasan na Argentina ya fara wasa a ranar.

“Leo zai buga wani bangare na wasan amma koci ne ke da wuka da nama kuma hakan ya dogara ne kan Leo idan ya ce a shirye yake domin mun san cewa ya shafe makonni da iyalansa amma yana kama da ya shirya kuma lafiyarsa kalau amma duk da haka yana bukatar lokaci ya saba,” in ji Beckham.

Beckham ne dan wasa mafi girma da ya koma gasar MLS inda ya saka hannu kan yarjejeniya da Galaxy a 2007 a lokacin da gasar League ke da kungiyoyi 13 kacal idan aka kwatanta da 29 da ake da su a yanzu kuma a lokacin tsarin wasan bai kai na yanzu kayatarwa ba.

AFP