Masana ƙwallon ƙafa da suka kalli wasan da Liverpool ta sha kaye a hannun Atalanta a gasar Europa matakin kwata-fainal, sun yi tsokaci kan rashin ƙoƙarin da 'yan wasan Liverpool suka nuna a wasan da aka tashi suna da ci 1-0.
Shafin Goal.com ya bai wa shahararren ɗan wasan gaba na Liverpool makin 4/10 kacal, yayin da shafin ESPN ya ba shi maki 6/10, saboda rashin taɓuka abin a-zo-a-gani.
Abin tambaya a nan shi ne me ke damun Mo Salah, tun bayan dawowarsa daga doguwar jinyar da ta sa ya baro gasar kofin ƙasashen Afirka ta AFCON ta bana?
Salah ne ya ci ƙwallo ɗaya tilon da Liverpool ta ci a zango na biyu na wasansu da Atalanta, ta hanyar bugun ɗurme. Sai dai bayan haɗa sakamakon wasan da na zangon farko da aka ci Liverpool 3-0, sakamakon ƙarshe ya zamo ci 1-3.
Masoya Liverpool sun yi zaton ƙwallon da Salah ya ci tun ana minti na 7 da fara wasan, zai saka musu ƙaimin ramakon ƙwallaye ukun da Atalanta ta ci su a baya, ta yadda za su iya juya akalar wasan har su nemi nasarar tsallakawa mataki na gaba a gasar ta Europa.
A baya dai, Liverpool ta sha raja'a kan zafin-nama irin na Salah don samun mafita sanda wasa ya ƙi musu kyau. Sai dai a wannan karon, Bamisiren ya gaza taimaka wa Liverpool ta kawo bantenta a birnin Bergamo na Italiya.
Salah da ma sauran 'yan wasan gaba na Liverpool irinsu Cody Gakpo da Luis Diaz sun gaza ciyo ƙarin ƙwallon don farke ƙwallaye biyu da ake binsu, yayin da wasan ya ƙarke a 3-1.
A wata gagarumar dama da ya samu kafin a tafi hutun rabin lokaci, Salah ya yi firi da mai tsaron ragar Atalanta, Juan Musso, amma sai ya caki ƙwallon ta tashi sama ta haure gefen hagu.
A ƙarshe dai an cire Salah a tsakiyar wasan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, inda Darwin Nunez ya maye gurbinsa a minti na 66. Haka wasa ya ƙare Liverpool sun ci wasa amma an ci su yaƙi.
Duk da cewa a yanzu Salah yana da ƙwallaye 24 a kakar bana a duka gasannin da ya buga, masu nazarin ƙwallon Liverpool sun bayyana cewa Salah bai dawo kan ganiyarsa ba tun bayan doguwar jinyar da ya yi, inda ya dawo wasa a farkon watan Maris.
Yanzu dai ta tabbata cewa kocin Liverpool Jurgen Klopp ba zai ci komai a gasannin Turai ba a kakarsa ta ƙarshe yana jagorantar kulob ɗin.
Babban aikin da ke gaban Klopp a yanzu shi ne ya maido da kuzarin tawagar tasa kafin wasansu na Lahadi da Fulham, domin ganin ko za su samu damar ci gaba da neman ɗaukar Kofin Firimiya na bana, idan suka iya hayewa gaban Man City da Arsenal.