An ceto mahaifiyar dan wasan Liverpool Luis Diaz daga hannun masu garkuwa da mutane ranar Asabar amma har yanzu ana neman mahaifinsa, a cewar shugaban kasar Colombia Gustavo Petro.
Petro ya wallafa sako a shafinsa na X, wanda a baya ake kira Twitter, cewa an ceto mahaifiyar Diaz a yankin Barrancas da ke arewacin Colombia.
"Muna ci gaba da neman mahaifinsa," in ji shugaban kasar.
Ofishin antoni janar na Colombia ya ce yana aiki tukuru kan batun.
"Daga lokacin da ofishin antoni janar ya samu labarin sace mahaifan dan wasan Colombia Luis Diaz a Barrancas ko La Guajira, tawagar kwararru ta masu shigar da kara da 'yan sanda da sojoji ta dukufa aiki domin gano inda wadannan mutane suke, da kuma gano wadanda suka sace su," a cewar sakon da ofishin ya wallafa a shafin X.
Kafafen watsa labarai na kasar sun ce Luis Manuel Diaz da Cilenis Marulanda sun je gidan mai ne yayin da masu garkuwa da mutane suka sace su.
Shugaban 'yan sandan kasar Janar William Salamanca, ya ce ya tura jami'an leken asiri da wasu jami'an tsaro domin kubutar da mutanen biyu.
Gwamnan La Guajira, Diala Wilches, ta yi tir da sace mahaifan dan wasan.
"Muna kira ga masu garkuwa da mutanen su sake su nan-take cikin koshin lafiya," in ji ta.
Dan wasan na Liverpool da Colombia, mai shekara 27, bai ce komai game da batun ba amma kungiyarsa ta fitar da sanarwa ranar Lahadi tana mai cewa tana "sane da abin da ke faruwa game da mahaifan Luis Diaz a Colombia".
"Muna fata za a warware matsalar cikin lumana kuma da wurwuri," kamar yadda kungiyar ta bayyana. "Kafin nan, kwanciyar hankalin dan wasan ita ce babbar damuwarmu."
Diaz, wanda ya buga wa Colombia sau 43, ya tafi Liverpool daga Porto a shekarar da ta wuce.