Dan wasan kwallon kafa na Liverpool Darwin Nunez / Hoto: AP

Darwin Nunez ya yunkuro da karfinsa a kakar wasa ta biyu da ya buga wa Liverpool, a cewar kocin kungiyar Juergen Klopp.

Dan wasan na kasar Uruguay ya zura kwallo a ragar West Ham United a fafatawar gasar Firimiya ta Ingila da suka yi ranar Lahadi inda suka tashi da ci 3-1.

Nunez, mai shekaru 24, ya zura kwallaye 12 sannan ya taimaka aka zura kwallaye hudu a wasanni 35 da ya buga tun bayan sayo shi da aka Liverpool ta yi daga Benfica a bara kan Euro 75m (dala miliyan 79.85).

Bayan irin rawar ganin da ya yi a bugun daga kai sai mai tsaron gida a kakar wasa ta bana, Nunez ya zura kwallaye uku sannan ya taimaka aka zura kwallo daya a wasanni shida da ya buga.

Ya kuma yi nasarar zura kwallo da taimaka wa Liverpool ta yi nasara a wasan da ta doke LASK da ci 3-1 a gasar cin kofin Europa League a ranar Alhamis.

"Ya yunkuro da karfinsa a makonnin da suka shude. Ya zama babban barazana," a cewar Klopp.

Ya kara da cewa ''A koyaushe Nunez na tare da mu, kuma hakan na da matukar muhimmaci a gare mu.''

Liverpool dai ta yi nasarar a wassanin da ta buga inda a yanzu take matsayi na biyu da maki biyu tsakaninta da Manchester City.

Za kuma ta karbi bakuncin wasan Championship na Leicester City a gasar cin kofin League a ranar Laraba, sannan kuma za ta buga gayyata na zuwa mataki na hudu da Tottenham Hotspur a ranar Asabar.

TRT Afrika