Duk da Kylian Mbappé ba ya buga wa Faransa a yanzu, ana sa ran ya zama wanda ya fi kowa ci wa ƙasar ƙwallo a nan gaba. / Hoto: AFP

Kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Faransa, Didier Deschamps ya ce shahararren ɗan wasan ƙasar kuma kyaftin, Kylian Mbappe yana fama da matsalar “rashin kuzari da tunani” yayin da yake fuskantar “matsanancin” yanayi a ƙungiyarsa ta Real Madrid.

Yayin da Mbappe ya gaza buga wa ƙasarsa wasa a karo na biyu a jere, hankali ya koma kan tauraron ɗan wasan wanda ake ganin yana fuskantar rashin kumari a ƙungiyarsa a Sifaniya.

Ɗan wasan wanda a bazarar nan da ta gabata ya koma ƙungiyar da yake burin bugawa wasa a Madrid, an yi zaton ya zama cikamakon ƙarfin Madrid. Sai dai bayan watanni, kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba.

Mbappe mai shekaru 25 ya ci ƙwallo guda ne kacal a wasanni bakwai na ƙarshe da ya buga wa Madrid. Sannan bai ciyo wa Faransa ƙwallo ba tun a watan Yuni.

A wasanni biyu da Faransa ta buga a baya-bayan nan, ba a kira Mbappe tawagar ba ba, ciki har da wasan da suka buga jiya Alhamis da Isra'ila wanda aka tashi 0-0.

Me kocin ya ce?

Da yake magana kan rashin kiran Mbappe, kocin Didier Deschamps ya ce, “A fili yake [Mbappe] yana cikin mawuyacin hali. A zahiri, yana cikin wani yanayi mara daɗi a rayuwarsa ta wasa.”

Deschamps ya ce game da rashin zuwan ɗan wasan gasar Nations League, “Ya so ya zo. Amma ina tunanin ya fi kyau gare shi [kar a kira shi] a yanzu. Kowa zai iya samun kansa cikin matsanancin yanayi. Akwai batun kuzari sannan akwai na tunani.”

A tarihin bugawa Faransa, Mbappe ya ci ƙwallaye 48 cikin wasanni 86, sannan ana sa ran zai zamo wanda ya fi kowa ciyo wa ƙasar ƙwallo a nan gaba.

A yanzu dai, Mbappe ya mai da hankali kan neman farfaɗowa daga halin rashin tagomashi da yake ciki a Real Madrid, yayin da za su buga wasa da Leganes ranar 24 ga Nuwamba a gasar LaLiga.

TRT Afrika