Yayin da ake ci gaba da cinikayyar 'yan wasa gabanin fara kakar wasanni ta baɗi, rahotanni sun nuna cewa Manchester United ta Ingila ta yanke shawarar sayar da ɗan wasanta da ya tafi Borussia Dortmund a matsayin aro.
An ruwaito sanannen ɗan jaridar nan mai ba da rahotannin ƙwallo, Fabrizio Romano, yana cewa Dortmund tana cikin ƙungiyoyin da ke da sha'awar sayen Sancho.
Sancho zai bar United gaba ɗaya, bayan kammala aron da ya tafi, ko da an samu canji a kocin United a kakar 2024-25, kasancewar ana tababa kan cigaba da zaman Erik ten Hag a matsayin manaja duk da cewa ya ci kofin FA na bana.
Da ma dai saɓanin da Ten Hag ya samu da Sancho shi ne babban dalilin da ya sanya ɗan wasan mai shekaru 24, ya tafi Dortmund tun a watan Janairu.
A zamansa a Dortmund, Sancho ya ci ƙwallaye uku da tallafin ƙwallo uku a wasanni 21 da ya buga a gasannin Bundesliga da na Zakarun Turai. United na fatan samun Fam miliyan £40m daga Dortmund ko sauran ƙungiyoyin da ke burin sayen Sancho.
Lukaku na shirin barin Chelsea
Kazalika, a wani rahoton daban daga Romano, Chelsea ta dage kan lallai sai an ba da kuɗin da ya kai Fam miliyan £38, kafin ta saki haziƙin ɗan wasan nan ɗan asalin Beligium, Romelu Lukaku.
Wannan na zuwa ne bayan kulob ɗin Napoli na Italiya ya nuna sha'awarsa kan Lukaku, bayan zuwan sabon koci Antonio Conte, wanda ya yi aiki da Lukaku, sanda yake jagorantar ƙungiyar Inter Milan.
Chelsea ta bayyana ƙarara cewa ba za ta bar Lukaku, mai shekaru 31 ya ƙara tafiya aro ba, bayan ya cika kakar wasa biyu a Inter Milan, da kuma Roma, duka a Italiya.
A Roma dai, Lukaku ya ci ƙwallaye 21 da tallafin ƙwallaye huɗu, cikin wasanni 47 a dukkan gasanni da ya buga.
Yayin da Chelsea ke neman Fam £38m kan Lukaku, Napoli ba za ta iya sayan sa ba, har sai idan Victor Osimhen ya bar kulob ɗin. Da ma ana alaƙanta Osimhen da komawa Chelsea.
Haka kuma, akwai ƙungiyoyin ƙasar Saudiyya da ke da sha'war sayan Lukaku. Amma dai tuni kocin Napoli, Conte ya ayyana aniyarsa ta sake aiki da Lukaku a Napoli.