Kylian Mbappe ya ce ya san haɗarin da yake fuskanta na ci gaba da buga wasa yayin da yake jinyar hancinsa da ya karye a gasar Euro 2024. / Hoto: Reuters

Kylian Mbappe, ɗan wasan Faransa da ke buga Gasar Kofin Ƙasashen Turai na Euro 2024 ya koka kan makarin fuskar da aka masa, don ya saka duk lokacin da zai buga wasa don baI wa hancinsa kariya.

Sau biyar ana sake ƙerawa da daidaita makarin fuskar da a yanzu Kylian Mbappe yake sakawa a yayin wasa, sakamakon raunin da ya samu a hancinsa a gasar da ke gudana a ƙasar Jamus.

A wasan Faransa da Austria ne aka doki Mbappe a fuska, inda ƙashin karan hancinsa ya farfashe. Amma ya ce, "Ban ɗauka wani babban rauni ba ne, ban san na karya hancina ba. Amma daga baya, na ɗauka zai tilasta min komawa gida".

Game da ƙirar makarin fuskar, Mbappe ya ce abin na takura masa. “Duk lokacin da wani abu ya faru a filin wasa, ina shan wahala saboda abin yana taƙaita min gani, kuma gumi yana taruwa a fuskata".

Raunin nasa ya hani shi buga wasan da Faransa ta kara da Netherlands, inda ya zauna a benci har aka tashi wasan. Amma a wasansu da Poland ya buga, har ma ya ci ƙwallo a bugun ɗurme.

"A yanzu ba ni da zaɓi, ba zan iya wasa babu makarin ba. Yana ba ni haushi. Amma ba dalili ne da zan ƙi farin ciki ba, saboda da shi ne kawai zan iya buga wasa. Don haka ina godiya da samun wannan makarin fuska,” in ji Mbappe.

Mbappe wanda ya koma buga wa Real Madrid wasa daga PSG, ya kuma ce yana tsoron ka da a ringa kai masa farmaki, daga 'yan wasan tawagar da za su tunkara.

Faransa na buƙatar Mbappe ya ci gaba da jan ragamar tawagarsu don neman sa'ar lashe kofi na bana, inda a yanzu yake shirin tunkarar wasansu da Belgium a matakin 'yan 16 na siri-ɗaya-ƙwale, wanda za a yi a birnin Dusseldorf.

TRT Afrika