Mahrez ya ci kwallo ta uku lokacin da kwace kwallon da Jack Grealish ya bugo ta wuce Wes Foderingham a minti na 66.

Riyad Mahrez ya samar wa Manchester City gurbi a wasan karshe na cin Kofin FA bayan ya zura kwallo uku shi kadai a ragar Sheffield United a wasan da suka tashi 3-0 a Wembley ranar Asabar.

Wannan ne karon farko da aka zura kwallo uku a zagayen dab da na karshe a gasar FA tun 1958.

'Yan wasan Sheffield United sun yi ta kokarin zura kwallo inda suka samu wata babbar dama ta hannun Iliman Ndiaye wanda ya cilla kwallon da golan City Stefan Ortega ya cafe. Daga nan Mahrez ya samu damar zura kwallo ta farko.

'Yan wasan City sun fuskanci matsaloli a mintunan farko na wasan inda 'yan wasan Paul Heckingbottom suka rika ba su wahala amma daga bisani sun samu dama bayan dan wasan Sheffield Daniel Jebbison ya farmaki Bernardo Silva inda Mahrez ya kara azama ya kara zura kwallo.

Mahrez ya ci kwallo ta uku lokacin da kwace kwallon da Jack Grealish ya bugo ta wuce Wes Foderingham a minti na 66.

TRT Afrika da abokan hulda