Marigayi Kobe Bryant/Hoto: AFP

Tsohon ɗan wasan ƙwallon kwando NBA kana mahaifin fitaccen ɗan wasa marigayi Kobe Byrant wato Joe Byrant da aka fi sani da Jellybean ya mutu yana da shekara 69 a duniya, a cewar sanarwar da Jami'ar La Salle ta fitar a ranar Talata.

Jellybean ya taka leda a makarantar Philadelphia daga shekarar 1973 zuwa 1975, sannan ya ba da horo kan wasan daga shekarar 1993 zuwa 1996.

Ya kuma shafe tsawon shekara tara yana buga wasan NBA wa ƙungiyar Philadelphia da San Diego Clippers da Houston Rockets da kuma ƙasashen Turai.

"Mun yi bakin cikin sanar da rasuwar babban ɗan wasan kwallon kwando na La Salle Joe Bryant," in ji sanarwar da makarantar ta Philadelphia ta fitar.

Sanarwar ta ƙara da cewa "Ya kasance mamba na ƙungiyar wasannin ƙwallon kwando kuma za mu yi matuƙar kewarsa sosai."

Fitaccen ɗan wasan kwallon kwando Kobe Byrant tare da Mahaifinsa Joe Byrant/ Hoto: AFP

Joe Bryant ya kasance ɗan wasan gaba da ya taka leda wa ƙasar Italiya a shekarar 1983 zuwa 1991 kafin ya yi ritaya daga wasan a ƙungiyar Mulhouse na Faransa a 1991.

Kobe Bryant, wanda aka haife shi a lokacin da mahaifinsa ke taka leda a shekarun 1976, ya kasance zakara a fagen wasannin NBA har sau biyar, kana ya lashe lambar yabo ta zinari sau biyu a gasar Olympics kuma ya zama dan wasa mafi daraja ta NBA a 2008 wanda ya kwashe tsawon rayuwarsa a wasan NBA daga shekarar 1996 zuwa 2016 yana taka wa ƙungiyar Los Angeles Lakers leda.

Fitaccen ɗan wasan Laker, Bryant ya mutu ne a haɗarin helikwafta a shekarar 2020 tare da ƴarsa Gianna, a lokacin yana da shekara 41.

AFP