Romelu Lukaku ya dade yana fuskantar miyagun kalamai na wariyar launin fata/ PHOTO: Reuters

Kamfanin da ke kula da lamuran Romelu Lukaku ya nuna bacin ransa game da yadda aka bai wa dan wasan Inter Milan katin gargadi na biyu da kuma jan kati don ya nuna wa magoya bayan Juventus da ke masa wakar wariyar launin fata yatsa.

Lamarin ya faru ne bayan Lukaku ya zura kwallo a raga da bugun fenareti a karshen wasa inda Inter Milan da Juventus suka tashi 1-1 a wasan kusa da na karshe na Gasar Kofin Italiya ranar Talata.

Lukaku ya saka yatsansa a lebansa kamar yana cewa mutanen su yi shiru bayan ya zura kwallon a raga.

Abin da Lukaku ya yi ya bata wa Juventus rai kuma fada ya kaure tsakanin ‘yan kungiyoyin biyu inda aka kori dan wasan gaba na Juventus, Juan Cuadrado, da golan Inter, Samir Handanovic.

"Kalaman wariyar da magoya bayan Juventus suka yi wa Romelu Lukaku a birnin Turin abin takaici ne kuma ba za a lamunce su ba," in ji shugaban Roc Nation Sports International, Michael Yormark .

"Kafin ya buga da lokacin da ya buga da kuma bayan ya buga fenaretin, an yi masa miyagun kalaman wariya. Romelu ya yi murnar zura kwallon a raga kamar yadda yake murnar cin kwallo a ko da yaushe," in ji shi.

Lukaku yana murnar zura kwallo a raga ne ta hanyar saka yatsa a lebansa/PHOTO: Reuters

Ladabtarwa

"Martanin alkalin wasan shi ne bai wa Romelu katin gargadi. Romelu ya cancanci Juventus ta nemi afuwa daga gare shi, kuma ina sa rai hukumar Gasar Kofin Lig ta yi Allah wadai da irin wannan dabi’ar ta magoya bayan Juventus nan take," kamar yadda Yormark ya fada.

"Dole hukumomin Italiya su yi amfani da wannan damar su dakile wariyar launin fata maimakon su hukunta wanda aka cutar."

Hukumar Gasar Lig ta Italiya ta fitar da wata sanarwa ranar Laraba inda ta yi "Allah wadai da dukkan wariyar launin fata da ko wace wariya." Sai dai ba ta ambaci sunan Lukaku ba.

"Mutane kalilan a cikin ‘yan kallo ba za su bata wasan kwallo ba kuma ba sa wakiltar tunanin dukkan magoya baya,” in ji hukumar.

Akwai yiwuwar alkalin Lig din ya fara shari’ar ladabtarwa a kan lamarin, yayin da Juventus ta ce za ta hada kai da hukumomi domin gano magoya bayan da suka aikata laifin.

An dade ana yi wa Lukaku kalaman wariyar launin fata saboda bakar fatarsa.