Kungiyar Manchester United ta sayi golan Inter Milan Andre Onana a kan euro 55m.
Kungiyar za ta biya dan wasan na kasar Kamaru €50million da kuma karin €5m na tsarabe-tsarabe.
United tana fatan dan wasan mai shekara 27 zai shiga cikin tawagarta a balaguron da za ta yi zuwa Amurka ko da yake sai sun nemar masa biza.
Kocin kungiyar Erik ten Hag ya soma neman daukar dan wasan ne a karshen kakar da ta gabata bayan ya yi aiki tare da shi a Ajax.
Ya ce Onana zai iya taka muhimmiyar rawa a United kuma ana ganin shirin daukarsa ne ya sa golan kungiyar David de Gea ya ki amincewa da sabuwar kwantaragin da kUnited ta yi masa tayi.
Onana ya kwashe shekara bakwai da rabi a Ajax kafin ya tafi Inter a watan Yulin 2022.
TRT Afrika da abokan hulda