Inter Milan ta yi babbar hobbasa ta samun gurbi a wasan karshe na cin Kofin Zakarun Turai bayan ta doke AC Milan a San Siro ranar Laraba da daddare.
A wasan da aka kwashe makonni ana hasashen yadda za ta kaya wanda 'yan kallo kusan 80,000 suka halarta, Inter ta soma wasan da kafar dama inda Edin Dzeko ya zura kwallo a minti na takwas da soma wasa.
Nan take kwallon ta sa jikin magoya bayan Milan ya yi la'asar.
Sun kara shan mamaki minti uku bayan haka inda Henrikh Mkhitaryan ya dirka musu kwallo a raga.
Duk kokarin da AC Milan suka yi na farke kwallaye biyun ya ci tura.
Yanzu Inter suna mataki mai karfi na isa wasan karshe na Zakarun Turai - inda za su fuskanci Manchester City ko Real Madrid - idan tagwayen Milan din suka sake haduwa a wasa na biyu na zagayen kusa da karshe ranar Talata 16 ga watan Mayu.
Sau uku Inter Milan suna lashe Kofin Zakarun Turai, sai dai yau shekara 13 rabon da suka kai wasan karshe inda suka daukin Kofin.