Rubiales, mai shekaru 46, da fari yana sukar masu tsangwamarsa, amma daga bisani ya nemi gafara, ko da yake an ce hakan bai wadatar ba. /Hoto Reuters

FIFA ta fara shirin daukar matakan ladabtarwa kan shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Sifaniya Luis Rubiales a ranar Alhamis, bayan da ya sumbaci ‘yar wasaan kasar Jenni Hermoso yayin wasan karshe na gasar kwallon kafa ta mata ta duniya.

Wata sanarwa da FIFA ta fitar ta bayyana cewa “Kwamitin ladabtarwa na FIFA ya sanar da Luis Rubiales, shugaban Kungiyar Kwallon Kafa ta Sifaniya cewa daga yau (Alhamis) za a fara bincike don ladabtar da shi kan abun da ya faru a yayin wasan karshe na gasar kwallon kafa ta mata.”

FIFA ta ce wannan abu “Zai iya saba wa sashe na 13 sakin layi na 1 da 2 na kundin dokar labadtarwa ta FIFA.”

“Yar wasan Sifaniya Hermoso ta fitar da sanarwar hadin gwiwa tare da kungiyar, wadda ta yi kiran da a dauki matakin ladabtarwa kan shugaban na RFEF.

Sanarwar ta ce “Muna aiki don ganin lallai irin wadannan ayyuka ba su wuce ba tare da fuskantar hukunci ba, mu tabbatar an hukunta su, kuma matakan da za a dauka su zama abun misali wajen kare mata ‘yan kwallon kafa daga ayyukan da ba su dace ba.”

Gasar zakarun Sifaniya ta Liga F ma ta fitar da sanarwa, inda ta yi kira da a kori Rubiales.

Rubiales, mai shekaru 46, da fari yana sukar masu tsangwamarsa, amma daga bisani ya nemi gafara, ko da yake an ce hakan bai wadatar ba.

TRT Afrika da abokan hulda