Jimillar kudin shiga da Liverpool ya samu ya yi daidai da na shekarar kudi ta baya, wato fam miliyan 594. / Hoto: Liverpool/X / Hoto: AFP

Kulob ɗin Liverpool FC na Ingila ya sanar da tafka asarar fam miliyan tara (dala miliyan $11.40) a shekarar kuɗi ta 2022-23, amma kuɗin shigar da ya samu daga kasuwanci ya ƙaru zuwa fam miliyan 272.

A sanarwar da kulob din ya fitar ranar Alhamis, kudin shigar da ya samu ya kai daidai da wanda ya samu a shekarar kudi da ta gabata, wanda ya kai fam miliyan 594, duk da kakar wasan ba ta yi wa kulob din kyau sosai ba sakamakon ƙarewa a mataki na biyar a Gasar Firimiya.

Kulob din, wanda Jurgen Klopp ke jagoranta an fitar da shi a Gasar Zakarun Turai ta UEFA a matakin 'yan-16 a shekarar 2023, sannan a shekarar 2022 an fitar da su ne a wasan karshe, a shekarar da suka ci gasar League Cup da FA Cup.

Sai dai sakamakon fitar da kulob din da wuri a gasannin cin kofunan gida a kakar bara ya haifar da rasa kudin shiga daga tikitin wasa da ya kai fam miliyan bakwai zuwa 80, yayin da kudin shiga daga midiya ya ragu da fam miliyan 19 zuwa 242.

Madogarar kulob

Babban manajan gudanarwar Liverpool, Andy Hughes ya ce, "Gudanar da wannan babban kulob a yanayin samar da kudi kuma bisa la'akari da manufofin kulob din shi ne abin da muka sa a gaba. Kamfanin FSG (Fenway Sports Group) ya sayi kulob din na Liverpool FC a 2010".

"Duk da hauhawar kudin gudanar da kwallon kafa a wannan zamani, nasarorin ayyukanmu na kasuwanci yana nuni da karfinmu da matakin kudi da muke kai, na cigaba da hawa yayin da muke gogayya a matakin kololuwa na kwallon kafa a duniya."

Hughes ya kara da cewa kammala aikin Anfield Road Stand a watanni masu zuwa zai habaka kudin shiga da ake samu a ranakun wasa, ganin yadda girman filin wasa na Anfield zai karu ya iya daukar 'yan kallo 61,000.

A lissafin shekarar kudin da ta gabata, kudaden gudanarwar kulob din sun ƙaru da fam miliyan 17 zuwa fam miliyan 562.

TRT Afrika