Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Al-Nassr da ke Saudiyya, ta gabatar da tayin sayen mai tsaron ragar Manchester City, Ederson, wanda ɗan asalin Brazil ne.
An ruwaito cewa Al-Nassr, wadda take da shahararren ɗan wasa Cristiano Ronaldo, ta gabatar da 'gagarumin tayi' na kwantiragin shekara biyu don kawo Ederson zuwa gasar Saudi Pro ta Saudiyya, daga gasar Firimiya ta Ingila.
Rahotanni sun ce tayin ya kai Fam miliyan 51m (dala miliyan 65). Da zarar Ederson ya amince da wannan tayin, Al-Nassr ta shirya tattaunawa da City don tabbatar da ya taho Saudiyya.
Al-Nassr ne neman maye gurbin mai tsaron gidanta na yanzu David Ospina, sakamakon cewa golan ɗan asalin Colombia ya kusa kammala kwantiraginsa.
Sai dai duk da cewa mataimakin Ederson a City, wato Stefan Ortega, yana ƙoƙari sosai, amma babu alamar kocinsa Pep Guardiola zai amshi tayin tafiyar babban golansa.
Ederson ya zo Manchester City ne daga Benfica a 2017. A bayan an ruwaito cewa City ba za su sayar da shi ba a farashin da ya gaza Fam miliyan 34 (dala miliyan 43). Sai dai samun wanda zai gaje shi a City zai iya musu wahala.
Kwantiragin Ederson a Man City ba za ta ƙare ba sai shekarar 2026.