Dan wasan gaban Nijeriya Sadiq Umar ya yi karin haske kan zargin da ake yi masa na kin buga wa kasar gasar AFCON da gangan ta hanyar fakewa da rauni.
A wata sanarwa da dan wasan gaban Real Sociedad din ya fitar a shafinsa na Instagram, ya bayyana cewa likitocin Super Eagles na Nijeriya sun gano yana da rauni a gwiwarsa sai dai daga baya da ya koma kulob din nasa, likitoci sai suka nuna kujewa ce kawai ya yi wanda hakan ya sa ya koma wasa.
“Ya zama wajibi a gare ni na yi magana kan sakonnin da na samu daga ƴan uwa ƴan Najeriya, inda suke zargina da fakewa da rauni domin barin kungiyar kwallon kafa ta kasa kafin gasar AFCON na koma kulob dina. Bayyana halin da ake ciki da kuma ba da cikakken bayani game da abubuwan da suka faru yana da muhimmanci,” in ji dan wasan mai shekara 26.
“A lokacin wasan sada zumunci da Guinea, na samu kalubale daga ‘yan wasan baya biyu na Guinea, wanda ya kai ga bugun fanareti ga Nijeriya. Duk da likitoci sun ba da shawarar cire ni daga wasan domin ba ni kariya, na dage kan ci gaba da buga wasa kuma na kammala wasan. Washe gari, sai gwiwata ta kumbura,” kamar yadda dan wasan ya kara da cewa.
“Tawagar likitocin Super Eagles sun gudanar da cikakken bincike, inda suka ce na samu ciwo a gwiwa. Sakamakon haka, sai kocin ya yanke shawarar maye gurbina bisa la'akari da rashin tabbas game da cancantar shiga AFCON.
“Bayan na dawo kulob dina ne aka yi min gwaje-gwaje sosai, sai tawagar likitocin ta nuna cewa na samu kujewa ne kawai, wanda hakan ya sa aka sallame ni na ci gaba da yin atisaye,” kamar yadda ya kara da cewa.