Tawagar kwallon volleyball ta kasar Turkiyya ta lashe gasar a karon farko a tarihi bayan ta doke Serbia 3-2 a wasan karshe na CEV Europe. / Hoto: AA

Turkiyya ta doke Serbia a Gasar Kwallon Volleyball ta Mata ta Turai, bayan sun kammala zagaye na biyar ranar Lahadi.

Tawagar kwallon volleyball ta mata ta Turkiyya ta yi nasara da ci 27-25, 21-25, 25-22, 22-25, da kuma 15-13 a fafatawar da suka yi a Brussels.

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jinjina wa tawagar bisa samun wannan nasara.

"Ina taya murna ga Tawagar Matanmu ta Kwallon Volleyball, the Sultans of the Net, bisa samun nasarar lashe Kofin Turai na CEV na shekarar 2023. Muna alfahari da ku," in ji Erdogan a sakon da ya wallafa a shafinsa na X.

An zabi Vargas a matsayin gwarzuwar 'yar wasa wato MVP

An zabi Melissa Vargas, wadda ta samu maki 41 a wasan karshe, a matsayi "Gwarzuwar 'Yar Kwallo ta Gasar Zakarun Turai."

Kazalika an zabi Vargas a matsayin 'yar wasan da ta fi daraja.

TRT World