Mutane shida aka yi wa shari'a kan zargin ƙoƙarin cutar Paul Pogba. / Hoto: Reuters

Wata kotu a birnin Paris ta yanke hukunci kan yayan mashahurin ɗan wasa Paul Pogba, mai suna Mathias Pogba, bisa zargin yunƙurin cutar ɗan wasan.

Kotun ta samu Mathias da laifin yunƙurin tatsar kuɗi daga tsohon ɗan wasan Juventus da Manchester United, inda ta ɗaure shi tsawon shekaru uku a gidan kaso.

An zargi Mathias tare da wasu abokan wasan yarinta na Paul Pogba kan neman dala miliyan $14 daga wajen Pogba a ƙarshen 2022.

Mai shekaru 34, Mathias zai kwashe shekara guda ne da wata na'urar warwaro a ƙafarsa mai iyakance inda zai yi yawo, maimakon a gidan yari, inda aka ɗage sauran shekaru biyun.

Paul Pogba mai shekaru 31, ya faɗa wa 'yan sanda a baya cewa wasu tsaffin abokansa na yarinta, ciki har da yayan nasa Mathias, sun nemi kuɗi a wajensa "saboda ba shi tsaro" cikin tsawon shekaru 13.

Matsalolin rayuwa

Pogba dai ya yi ta shiga ƙalubale a rayuwar, inda ya taɓa faɗa a 2023 cewa ya yi tunanin barin ƙwallo kacokan, saboda matsin lambar da ya shiga sakamakon neman kuɗin nasa.

A yanzu dai Pogba na shirin dawowa buga ƙwallo bayan yin wa'adin dakatarwar da aka masa saboda kama shi da laifin shan ƙwayoyin ƙara kuzari.

Pogba zai iya komowa ƙwallo a Maris na 2025 bayan an rage wa'adin dakatarwar daga shekaru huɗu zuwa watanni 18 a shekarar nan.

A yanzu Pogba ba shi da kulob, bayan da ƙungiyar da yake buga wa wasa kafin dakatarwarsa, Juventus ta Italiya ta soke kwantiraginsa.

Ɗan wasan da ya taɓa lashe kofin duniya da Faransa, zai yi fatan samun ƙungiyar da za ta ɗauke shi wasa, kasancewar yana da sauran ƙwari a filin wasa.

TRT Afrika