De Gea ya soma wasa a United tun a 2011. Hoto/Reuters

Golan Sifaniya David de Gea, ya sanar da cewa zai bar Manchester United bayan shafe shekara 12, inda ya ce “lokaci ya yi da ya kamata ya fuskanci sabon kalubalen rayuwa”.

Golan mai shekara 32 wanda ya ci kyautar safar hannu ta gwal a Gasar Firimiya ta bara a matsayin wanda ya fi tare kwallaye a kakar bara, ya sha caccaka kan manyan kurakuran da ya rinka tafkawa a makon karshe na gasar.

Kwanitraginsa da Manchester United ya zo karshe ne a watan Yuni, inda ba a cimma wata yarjejeniya ta sake sabunta ta ba duk da tattaunawar da aka rinka yi a cikin kakar.

Ana rade-radin cewa United din na son daukar golan Milan Andre Onana.

A wani sako da ya wallafa a kafar sada zumunta, De Ge ya gode wa masoyansa na United kan irin goyon bayan da suka ba shi.

Sa’annan ya ce Manchester United za ta ci gaba da zama a cikin zuciyarsa.

A lokacin da kwantiraginsa ya kare a Juma’ar da ta gabata, United ta ce tana ci gaba da tattaunawa da dan wasan na Sifaniya.

De Gea ya soma taka leda a Atletico Madrid, amma Manchester United ta siye shi kan fam miliyan 18.9 a 2011.

Sa’annan kuma ya shafe shekara 12 a United inda ya yi wasa 545.

AFP