Hannayen-jarin Manchester United sun fadi da kasa da $700m a kasuwar hannun-jari ta New York ranar Talata bayan kafafen watsa labaran Birtaniya sun rawaito cewa an dakatar da shirin sayar da kungiyar.
Rahotanni sun ce mutanen da suka mallaki United, iyalan Glazer, sun cire kungiyar daga kasuwa bayan an gaza samun wadanda za su sayi kungiyar a farashin da suke nema, kamar yadda jaridar Daily Mail ta rawaito.
Ranar Talata, hannun-jarin kungiyar ya fadi da kashi 18.22 a kwana daya kacal -- faduwa mafi girma da aka taba fuskanta tun da aka sanya ta a kasuwa a 2012.
A cewar kakafen watsa labaran Birtaniya, mutum biyu da ke kan gaba wajen neman sayen kungiyar -- attajirin Birtaniya Jim Ratcliffe da Sheikh Jassim Bin Hamad Al Thani -- sun taya United a kan kimanin fam biliyan biyar, wato kusan $6.3b.
Iyalan Glazers su ne suka mallai kashi biyu cikin uku na kungiyar amma su suke da kusan dukkan iko na kungiyar.
Yanzu haka darajar Manchester United a kasuwar hannayen-jari ba ta wuce $3.15b ba, kasa rabin $7.5 b da iyalan Glazers suke so su sayar da kungiyar.
Bayanan da shafin 90min da ke harkokin kwallon kafa ya wallafa sun ce har yanzu ana tattaunawa domin sayar da kungiyar, inda ya ambato wasu majiyoyi na kusa da iyalan Glazers da kuma masu neman sayen United.