Premier League - Leeds United v Liverpool / Hoto: Reuters

Daga Mazhun Idris

A ranar Litinin ne Liverpool ta ci Leeds United zunzurutun kwallaye har shida, inda aka tashi shida da daya a wasansu na 30 a Gasar Firimiya.

‘Yan wasan gaba su biyu Mohamed Salah da Diogo Jota suka ci kwallaye biyu-biyu, yayin da Cody Gapko da Darwin Nunez suka ci daya-daya.

Jurgen Klopp, wanda yake a shekararsa ta takwas a matsayin manajan Liverpool ya ce bayan wasansu, “Ina ganin wannan shi ne mafi kyawun wasanmu a wannan kakar.”

Zuwa yau, lissafi ya nuna kofin Firimiya ya riga ya kubucewa Liverpool a bana, saboda ko sun ci duka wasanninsu da suka rage ba za su kamo Arsenal mai maki 73 ba.

Bari mu duba wasu alkaluma da za su nuna yadda Liverpool ke tsilla-tsilla a gasar Firmiyar bana ta kakar 2022-2023, da kuma wasu gasannin.

Liverpool mai abin mamaki

Liverpool na mataki na takwas a teburin Firimiya a kakar bana, duk da suna da kwantan wasa daya a hannunsu. Suna da jimillar maki 47 daga wasanni 30.

A yawan cin kwallaye, Liverpool ce ta hudu da kwallaye 56, yayin da Arsenal da Man City da Tottenham ne kawai suka fi ta yawan zura kwallaye. Dan wasanta Mohamed Salah shi ne na hudu a cin kwallo da kwallaye 15.

Zura kwallaye rigis a wasa daya ba sabon abu ba ne ga kulob din. Hasali ma a bana, Liverpool ne ke da kambun zura zunzurutun kwallaye a gida da waje. A gida sun ci Bournemouth 9-0 a waje kuma sun ci Leeds 6-1.

A karawarsu da Manchester United a farkon watan Maris, sun zura musu kwallaye har bakwai ba tare ramawa ba. Wannan ci shi ne mafi muni a tarihin Man United, kuma sau uku kacal aka taba musu hakan a baya.

Sai dai kuma, Liverpool ba su fara wannan kaka da abin a zo a gani ba. Wasansu uku na farko sun yi duro sau biyu, sannan a na uku Manchester United ta ci su 2-1.

Haka abu ya yi ta tafiya, yau a ci su, gobe su ci, jibi su yi kunnen doki. A wasansu shida na baya-bayan nan a gasar Firimiya, raba daidai suka yi, wato sun ci biyu, sun yi duro biyu, sannan an ci su sau biyu.

Idan aka duba wasanninsu 10 na karshe kuwa, inda suke da damar tattara maki 30, za a ga cewa wasa biyar suka ci, inda suka hada maki 18 suka barar da 12.

Haka nan idan aka duba wasannin 10 na kwanan nan wanda suka buga a gida, sun ci bakwai ne, sauran kuma aka ci su ko suka yi duro.

Idan aka juya akalar lissafin kuwa, a wasannin da suka buga a waje, wasa uku kacal suka ci, inda a sauran bakwai din kuma ko dai aka ci su, ko suka yi duro.

Farfadiya ko tsilla-tsilla

Wata kididdigar da ke nuna tsilla-tsillar Liverpool a kakar bana shi ne sau uku kacal suka taba jera wasanni suna yin nasara. Amma kuma, sau uku din suka taba jera wasannin suna shan kashi.

A tarihi, Liverpool ne kulob na biyu a Ingila wanda ya fi jera wasanni ba tare da an yi nasara kansa ba, inda ya yi wasa 44 tsakanin shekarar 2018-2020.

Zuwa yanzu dai, Liverpool sun buga wasanni 30, nasara 13, kunnen doki 8, sai rashin nasara 9. A lissafi, sun ci jimillar maki 47, wato maki 1.57 suke samowa a duk wasa.

Liverpool sun ci wasanni tara a gida, an ci su takwas a waje. Kuma sun hada maki 31 a gida, yayin da suka had maki 16 a wasaanin waje.

Duka-duka dai kwallaye 56 suka zura a wasanni 30, bayan da aka zura musu kwallaye 36 karkashin jagorancin babban mai tsaron raga Alisson Becker.

Zuwa yau, da ma dai an fitar da Liverpool daga gasar Zakarun Turai tun a zagayen kungiyoyi 16, inda Real Madrid ta doke su da jimillar kwallaye 6-2.

A gasar EFL ma an fitar da Liverpool a zagaye na hudu, kamar yadda a zagaye na hudun aka fitar da su a gasar FA Cup.

Yayin da Liverpool za ta buga wasa na gaba da Nottingham Forest ranar Asabar mai zuwa, za a jira a ga ko za su iya kai wa cikin biyar na farko a teburin Firimiya, don samun damar taka leda a Turai a badi.

TRT Afrika