Ten Hag  ya yi kokarin nuna cewa komai yana tafiya daidai a kungiyar / Photo: AP

Kocin Manchester United Erik ten Hag ranar Juma'a ya ce kungiyarsa tana fadi-tashin ganin lamuranta sun inganta a kakar wasan bana bayan da ta fara kakar da kafar-hagu.

Red Devils sun sha kashi a wasanni hudu cikin shida da suka buga a dukkan gasar da suka yi zuwa wannan lokaci, lamarin da ya zama babban kalubale a gare shi wata daya bayan soma kakar wasan.

United za ta je Burnley ranar Asabar don fafata da ita a yayin da take matsayi na 13 a tebirin Gasar Firimiya -- ta sha kashi a wasanni 18 a cikin wasanni 35 da ta buga ba a gidanta ba a dukkan gasa.

"Wannan ce shekarata ta biyu," a cewar Ten Hag, wanda kungiyarsa ta gama kakar wasan da ta gabata a mataki na uku a teburin firimiya.

"Na san ba kowanne lokaci ake samun abin da ake so ba -- za ka fuskanci koma-baya amma za ka koma kan ganiyarka muddin kuka hada gwiwa da 'yan wasanka, kuma abin da muke yi yanzu kenan.

Labaran da ke fitowa daga kungiyar na nuna cea mutane ba sa jin dadin abin da ke faruwa sannan ana tantama kan kwazon 'yan wasa.

Sai dai Ten Hag ya yi kokarin nuna cewa komai yana tafiya daidai a kungiyar a yayin taron manema labaran da ya gudanar, yana mai cewa: "Ban san wanda ya tsegunta wannan magana ba, amma ina sane da ra'ayin kowa, na san 'yan wasana. Kowa zai iya tofa albarkacin bakinsa, ba mu da matsala da hakan."

United tana fuskantar matsala ta 'yan wasan da ke jinya, abin da ya sa ake zaman dar-dar game da tafiyar da za ta yi zuwa Burnley, domin kuwa Jadon Sancho ba zai buga wasan ba bayan ya samu rashin jituwa da kocinsu.

AFP