Dan wasan Faransa Benzema ya nuna goyon bayansa ga Falasdinawa da kuma nuna kyamarsa ga yadda Isra'ila take ci gaba da musgunaw musu. / Hoto: Reuters

Karim Benzema ya gurfanar da Ministan Harkokin Cikin Gida na Faransa Gerald Darmanin a gaban kotu bisa zargin bata masa suna bayan da a bara ya yi zargin cewa tsohon dan wasan na Real Madrid yana da alaka "mai girma" da Kungiyar 'Yan'uwa Musulmai.

Takardun karar da Hugues Vigier, lauyan Benzema ya shigar ranar Talata sun bayyana cewa zargin da ministan ya yi masa sun "zubar da kimar" dan wasan, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito.

Ya gurfanar da ministan ne a Kotun Cour de Justice, wadda ita ce kadai take da ikon hukunta jami'an gwamnatin kasar bisa aikata laifi a yayin da suke gudanar da ayyukansu.

Benzema, wanda Musulmi ne kuma yanzu yana murza leda a kungiyar Al Ittihad ta kasar Saudiyya, ya ce ba shi da "alaka ko kadan da Kungiyar 'Yan'uwa Musulmai, kuma ba shi da dangantaka da kowane dan kungiyar".

Ya kara da cewa: "Ina sane da yadda ake amfani da matsayina na shahararren mutum wajen cim ma bukatu na siyasa, wadanda suka dauki sabon salo tun bayan ranar 7 ga watan Oktoba."

Darmanin, mai tsattsauran ra'ayi da ke son zama shugaban Faransa, ya soki Benzema bayan tsohon dan wasan na Faransa wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or ta 2022 ya wallafa sako a shafinsa na X a tsakiyar watan Oktoba inda ya nuna goyon baya ga Falasdinawan Gaza da aka mamaye.

A sakon nasa, ya ce bai kamata Isra'ila ta "rika yin musu luguden wuta ba".

TRT Afrika da abokan hulda