Martin Ndtoungou ya jagoranci tawagogin ƙwallon ƙafa na Kamaru a lokuta da dama baya. / Photo: AFP 

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Kamaru wadda ake kira da FECAFOOT ta ajiye batun naɗa ɗan ƙasar Belgium Marc Brys da gwamnatin ƙasar ta yi, inda ta maye gurbinsa da Martin Ndtoungou, a matsayin kocin wucin-gadi.

Sanarwar hukumar ta nuna cewa sabon kocin na riƙo shi ne zai jagoranci tawagar ƙasar a wasannin da za a yi a wata mai zuwa, na neman gurbin shiga gasar ƙwallon ƙafa ta duniya na 2026.

Matakin na zuwa ne bayan zazzafan ce-ce-ku-ce tsakanin Brys da shugaban hukumar, Samuel Eto’o ranar Talata. Wannan ya faru ne sakamakon tataɓurza tsakanin Eto'o da kocin, wanda ma'aikatar wasanni ta ƙasar ta naɗa a watan Afrilu, ba tare da amincewar Eto’o ba.

Bayan an gayyaci Brys tattaunawa ranar Talata, an hana da yawa daga jami'an da ke taimaka masa, waɗanda su ma ma'aikatar wasannin ta naɗa su, shiga ginin hukumar a Yaounde.

Daga baya Hukumar FECAFOOT ta kira taron gaggawa na kwamitin gudanarwarta, wanda suka yanke hukuncin yin sauyin.

Arangama

Wannan hukunci zai iya haifar da Eto’o ya sa ƙafar wando ɗaya da hukumar wasannin, wadda zuwa yanzu ta doge kan matsayinsu na naɗa Brys, duk da boren da hukumar ƙwallon ta yi.

Yadda aka saba gani dai, hukumar ƙwallo ce ke naɗawa da biyan koci, amma a wasu ƙasashen Afirka gwamnati ce ke yin hakan, musamman idan hukumar ƙwallon ba ta da kuɗi.

Tawagar Kamaru tana da maki huɗ daga wasanni biyu na farko na neman gurbi da suka buga, sannan za su karɓi baƙuncin Cape Verde ranar 8 ga Yuni, kwana uku daga nan sai su je Angola wasan gaba.

A wasannin neman gurbin, tawagogin da suka zo na farko a rukunoni tara masu tawagogi shida-shida, su ne za su buga gasar ƙwallon ta duniya da za a yi a ƙasashen Amurka, Canada da Mexico a 2026.

TRT Afrika