Tsohon gwarzon ɗan damben boksin na duniya Anthony Joshua ya doke Francis Ngannou sau uku a zagaye biyu da suka fafata a filin wasa na Kingdom Arena a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya ranar Asabar lamarin da ya ƙara masa tagomashi a fagen boksin.
Joshua, ɗan ƙasar Birtaniya da ke da tsatso a Nijeriya ya doke Ngannou, haifaffen ƙasar Kamaru mai shekara 37.
Karawar da aka yi mai taken "Knockout Chaos" a Turancin Ingilishi ta ƙayatar da ƴan kallo inda Joshua ya buge Ngannou.
Alƙalin wasan ya yi gaggawar shiga tsakanin inda ya tsayar da wasan sannan ya ayyana Joshua a matsayin wanda ya yi nasara bayan ya bubbuge Ngannou.
Masu kallon sun yi tsamanin Ngannou zai yi kataɓus a wasan bayan ya doke tsohon gwarzon ɗan wasan boksin Tyson Fury a fafatawar da suka yi a Riyadh a watan Oktoba, amma sai ga shi Joshua ya murƙushe shi.